5 Agusta 2021 - 11:45
Sudan Na Shirin Zama Mamba A Kotun ICC

Majalisar ministocin Sudan ta amince da wani kudiri da zai sanya kasar zama mamba a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya cewa da (ICC).

ABNA24 : An amince da kudirin ne yayin da ake shirin yin wata ganawa tsakanin ministoci da kuma tawagar shugabannin kasar.

Ana dai ganin wannan na kara matso Sudan, daga yunkurin da take na mika tsohon shugaban kasar Omar Hassan Al’Bashir, da kotun ke nema ruwa a jallo bisa zargin aikata laifukan yaki a yankin Darfur.

342/